An karrama BM Dzukogi a taron KAPFEST

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Marubuta waƙoƙin turanci, da littattafan adabi na gudanar da wani babban taro na ƙasa da ƙasa a Kano wanda ya mayar da hankali wajen ƙarfafa gwiwar masu fasaha da ƙirƙira don su yi amfani da basirar su wajen kira a samar da canji a cikin al’umma.

Daga cikin abubuwan da aka tsara gudanarwa a taron na kwanaki uku akwai tattaunawa da nazari daga manyan baƙi da aka gayyato daga jihohi daban-daban game da irin gudunmawar da suke bayarwa ga cigaban adabi, ilimi, da zamantakewa.

Shugabar taron Nasiba Babale ta buƙaci mahalarta taron su sauke nauyin da ke kansu, wajen isar da saƙon fatan samun canji, da gyara game da al’amuran da suke faruwa a ƙasar nan, zaman lafiya da tsaro.

smart

Ta ce, ‘A gaskiya jama’a da dama na cikin ƙunci, ana fuskantar ƙalubale mai yawa, ya kamata shugabanni da sauran ýan Nijeriya su yi wani abu don sauƙaƙa halin da ake ciki, kuma haƙƙin kowa ne ya ba da gudunmawa.’ 

Taron ya karrama fitaccen marubucin nan BM Dzukogi daga Jihar Naija, bisa irin gudunmawar da yake bai wa adabi fiye da shekaru 25, tare da tallafawa matasa masu basirar rubutun waƙoƙi da adabi, ba a Jihar Naija kaɗai ba har ma a Nijeriya bakiɗaya. 

A jawabin sa na godiya ga masu shirya taron da sauran mahalarta, BM Dzukogi ya bayyana fatan matasa masu tasowa za su yi amfani da basirar su wajen ganin ƙasar nan ta gyaru. A cewar sa, ‘Duk da kasancewar sa dattijo, amma na fitar da rai kan cewa dattijan ýan siyasar ƙasar nan suna da sauran wata basira ta kawo canjin da al’umma ke kwaɗayin samu. 

Wannan shi ne karo na biyu da ake shirya wannan taro na baje-kolin basirar matasa kan ƙirƙira da fasahar waƙoƙi, ƙarƙashin ƙungiyar Poetic Wednesday. An fara bikin da raye-rayen al’adun gargajiya da ziyarar wuraren tarihi kuma za a kammala da gasar ƙirƙirar waƙen baka, da ake sa ran ba da kyautar Naira Miliyan ɗaya. 

By ukarofi