‘
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar da sanarwar a Katsina.
Ya ce ‘yan sanda da ke zirga zirga a bisa manyan hanyoyin jihar suka kama Mubarak Bello da shekara 38 da ke zaune a unguwar kofar Yamma a ƙaramar hukumar kurfi a cikin wata mota kira Toyota Corolla lambar Legas.
DSP Sadiq ya ce bayan da ‘yan sanda sun bincike motar wanda a ke zargi sai suka gano bindiga kirar gida guda ɗaya da albarusai masu yawa a cikin motar.
“Haka kuma da suka faɗaɗa bincike a cikin motar sun gano katin shedar aiki na ɗan sandan bogi da lambar wata mota ta Kano”inji DSP Sadiq Aliyu.
Ya tabbatar da cewa yanzu haka wanda ake zargi yana hannun su suna faɗaɗa bincike domin gano yadda akayi ya mallaki waɗannan kayayyaki.
DSP Sadiq Aliyu ya ce da zarar an kammala bincike za a gurfanar da Mubarak a gaban kuliya.
