Gwamnatin Katsina ta biya diyyar aikin hanya ta biliyan N1.56

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mutane 376 ne suka amfana da waɗannan kuɗaɗe a matsayin diyyar wurarensu da za a gina tagwayen hanyar Kofar Sauri – Shataletalen Babban Masallacin Juma’a na Katsina.

Wannan hanyar na daga cikin hanyoyi 12 da gwamnatin Malam Dikko Raɗɗa ta ƙudiri aniyar faɗaɗawa ƙarƙashin shirin sabunta Jihar Katsina.

Kwamishinan ma’aikatar ƙasa da tsare-tsare ta Jihar Katsina Dr. Faisal Umar Kaita tare sauran masu ruwa da tsaki suka miƙa chakin kuɗaɗen ga waɗanda suka amfana da kuɗaɗen.

Dr. Faisal Umar Kaita ya ce ya zuwa yanzu gwamnatin Malam Dikko Raɗɗa ta kashe kuɗi sama da Naira N7.6 biliyan.

Dr. Kaita wanda ya ce wannan ayyuka na da nufin yiwa Jihar Katsina mafita mai ɗorewa, ya yi roƙon goyon bayan al’umma ga gwamnatin Malam Dikko Raɗɗa don haƙanta ya cimma ruwa.

Ya tabbatar da cewar, Gwamna ya bayar da umurnin biyan duk wanda aka taɓa wurinsa da darajar da zai iya samun madadi.

Tunda farko sai da mai riƙon kujerar babban sakataren ma’aikatar ƙasa da tsare-tsare, Alhaji Dikko Bala ya faɗi irin ƙudirin da gwamnatin Malam Dikko Raɗɗa ta ke da shi na ganin ana biyan mutane kuɗaɗen diyar wuraren su kafin fara aiki.

Ɗan Majalisar Dokoki mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina Aliyu Abubakar Albaba da Shugaban ƙaramar hukumar Katsina, Isah Miqdad,sun yaba a kan ɗimbin ayyukan raya ƙasa da ake yi yankin.

By ukarofi