Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Wata Mujallar Ilimi ta karrama shugaban kamfanin motoci na YIL, Alhaji Ya’u Abdullahi bisa gudunmuwar da yake bayarwa ga bunƙasa ci gaban matasa.
Wanda ya miƙa karramawar a madadin hukumar gudanarwa na Mujallar Abubakar ya ce karrawar ta zo ne bisa la’akari da aka yi da irin ɗimbin gudunmawa da Alhaji Ya’u Abdullahi ke bayarwa akan tallafawa matasa su koyi ayyuka na gyara da haɗa motoci.
Shi ma a nasa ɓangaren bayan karɓar shaidar karramawar shugaban kamfanin na YIL Alhaji Ya’u Abdullahi ya nuna matuƙar farin cikinsa da kuma godiya ga Allah bisa ganin irin wannan gudunmawa da yake bayarwa har aka karrama shi.
Ya ce suna gudanar da harkar gyara motoci da sauyawa musu tsari daga tuƙin dama zuwa tukin hagu da kuma yi mata filla-filla da haɗawa da sake musu yanayi har ma suna sayarwa..
Ya ce sun yaye matasa da dama da suka koyi aiki a wajen nasu sannan yanzu haka ma suna da ma’aikata kusan 40 ciki har da masu buƙata ta musamman da ɗaya daga cikknsu da gurgune da yake dogarawa da sanda sanda ya samu ƙwarewa a fannin ayyuka da dama da suke.
Alhaji Ya’u Abdullahi ya ce a shirye suke idan gwamnati za ta riƙa kawo musu matasa su riƙa koya musu sana’o’i sannan kuma ta riƙa tallafa musu wajen domin samun cigaba da inganta sana’ar su.
Shugaban na YIL Motors, Alhaji Ya’u Abdullahi ya ce wannan karramawar da Mujallar “Education Gallery” ta yi masa na ƙarin ƙaimi ne domin cigaba da koyawa matasa aikin domin ya zame musu mataki na sana’ar dogaro da kai.
Shi ma manajan wajen aikin motoci na YIL Lawwasu Umar ya ce sama da shekaru 17 ake gudanar da ayyuka na gyaran motoci a ƙarƙashin jagorancin Alhaji Ya’u Abdullahi kuma yana baiwa ma’aikata kulawa da ya kamata an kuma an yaye mutane da dama da suka koyi aiki a wurin.
Shi ma ɗaya daga ma’aikatan wajen Idris Ibrahim Abubakar ya ce da aikin gwamnati yake amma ya bari ya zo ya koyi sana’a na gyara motoci a kamfanin Alhaji Ya’u Abdullahi da shi ya dogara yake kula da kansa da iyalinsa fiye da lokacin da yake aikin gwamnati.
