
Yayin da ake cigaba da ƙoƙarin shawo matsalar ta ƙaddamar da ke tsakanin masu ruwa da tsaki a harkar fetur, ya yammacin jiya Litinin aka tashi baram-baram a wajen taron tattunawar sulhu da aka yi tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC da kuma wakillan kamfanin Ɗangote.
Kungiyar ma’aikatan dakon man fetur da iskar gas ta NUPENG ce ta yi barazanar shiga yajin aiki sakamakon matakin da kamfanin mai na Dangote ya dauka na fara jigilar mai zuwa gidajen mai.
Ministocin ƙwadago biyu ne suka shiga tsakani domin ganin an samu warware matsalar da ta taso tsakanin ɓangarorin, saidai kuma ba a samu galaba ba.
Kwamared Nuhu Abbayo Toro, shi ne babban magatakar na kungiyar kwadago ta TUC a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa babu wani da aka cimma a wajen taron sulhun.
Ya ce ” Tun da magana ce ta hakkin ma’aikata da kamfanin Dangote ke kokarin tauyewa, mun iya bakin kokarinmu don a samu masalaha amma ba a yi galaba ba.”
Kwamared Toro, ya ce” A don haka mu yanzu muna kan bakarmu ma’aikata zamu ci gaba da zaman ko ta kwana har illa masha Allahu.”
“Ina so na sanar da mutane abu guda wato ba gudu ba já da baya domin akan hakkin ma’akaci guda sai yadda karfin kungiyoyin kwadago ya kare.” In ji shi.
Kwamared Nuhu Abbayo Toro, ya ce,”Batun tsunduma yajin aiki a sanya ido aga abin da zai biyo baya.”
Kungiyar ta NUPENG, ta ce muddin matatar mai ta Ɗangote ta fara jigilar mai zuwa gidajen man da ke jihohi, to dubban ma’aikatan da ke aiki a depo-depo da kuma direbobin da ke tuƙa manyan motoci sama da 30,000 za su rasa aikinsu.
Ita ma ƙungiyar masu gidajen mai da iskar gas NOGASA, ta nuna goyon bayanta a kan matakin da NUPENG din ta ce za ta ɗauka na shiga yajin aiki.
Saidai, ƙungiyar masu gidajen mai da iskar gas ta arewacin Nijeriya (AROGMA) ta ce tana maraba da matakin da matatar Ɗangote ta ɗauka na yin dakon mai zuwa gidajen mai a faɗin ƙasar, kamar yadda BBCHausa ta ruwaito.
Jaridar ta kuma ruwaito akwai rahotannin da ke cewa ma’aikatan ƙungiyar ta NUPENG sun fara rufe wasu gidajen mai a arewacin Najeriya a matsayin martani ga kamfanin na Dangote.
