Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da dawowar Sanata Natasha duk da kammala dakatarwar wata shida

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da buƙatar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na ta dawo bakin aiki, inda ta ce har yanzu dakatarwar da aka yi mata na wata shida bai ƙare ba har sai Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yi hukunci akan lamarin.

Akawon riƙo na Majalisar Dokoki ta Ƙasa, Dakta Yahaya Ɗanzaria ya bayyana haka a wata takarda.

Ya bayyana cewa, Majalisar Dattawan tana sane da saƙon sanar da shirin Natasha na komawa bakin aiki a ranar 4 ga Satumba, 2025 inda ta kafa hujja ƙarewar wa’adin dakatarwar da aka yi mata.

Saidai ita majalisar ta ce duk da cewa dakatarwar ta fara aiki ne a ranar 6 ga watan Maris, 2025, al’amarin ya sauya kasancewar an miƙa shi ga Kotun Ɗaukaka Ƙara, wadda a yanzu ita ke da ikon yin hukunci a kai.

An dakatar da Akpoti-Uduaghan, wadda ke wakiltar Kogi ta Tsakiya daga harkokin majalisar ne a sakamakon saɓa wa dokokin tsayuwa a zauren majalisar.

Akan haka ne Natasha da kanta ta shigar da ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙarar domin duba halascin dakatarwar da aka yi matan.

A ranar 23 ga Satumba, 2025 Majalisar Dattawan za ta koma aiki bayan tafiya hutu da ta yi a baya.

By Babaji