An kashe mutane 155 ta hanyar ɗaukar doka a hannu cikin shekaru 10 a Nijeriya – Amnesty

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International Nigeria ta nuna matuƙar damuwa kan yawaitar kashe-kashen jama’a ta hanyar ɗaukar doka a hannu a ƙasar nan, inda ta bayyana cewa ta tattara aƙalla mutane 155 cikin shekaru 10 da suka gabata aka kashe.

Daraktan ƙasa na Amnesty International, Isa Sanusi, ne ya bayyana hakan yayin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Kano a ƙarƙashin gangamin Dakatar da Kisan Jama’a (End Mob ɓiolence Campaign).

Sanusi ya ce bayanan da da aka tattara sun haɗa da kashe-kashe da suka samo asali daga zargin ɓatanci ga addini, sata, da kuma maita, inda yawanci ake kai wa waɗanda ake zargi hari tare da kashe su ba tare da bincike ko bin ƙa’ida ta shari’a ba.

A cewarsa, rahotannin Amnesty International sun nuna cewa mutane 23 aka kashe a ‘yan shekarun nan sakamakon kisan jama’a a sassa daban-daban na ƙasar.

Ya jaddada cewa kisan jama’a ta hanyar ɗaukar doka a hannu ba matsalar yanki guda ba ce, domin an samu irin waɗannan abubuwa a dukkan yankunan Nijeriya, yana mai gargaɗin cewa ci gaba da amincewa da “ɗaukar doka a hannu” na barazana ga bin doka da oda.

Sanusi ya ɗora laifin yawaitar kisan jama’a kan raunin hukumomin tsaro da rashin amincewar jama’a da tsarin shari’a, inda ya ce mutane kan ɗauki doka a hannunsu idan suka yi zaton masu laifi za su tsira ba tare da hukunci ba.

Ya buƙaci gwamnatin Nijeriya da ta gaggauta ƙarfafa hukumomin tsaro da tsarin shari’a domin tabbatar da adalci da dawo da amincewar jama’a, yana mai jaddada cewa adalci mai inganci ne kawai zai iya kawo ƙarshen kisan jama’a a Nijeriya.

By ukarofi