Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Malam Muhammadu Sanusi II, ya naɗa Barham Amadu Husaini Yahaya a matsayin Sarkin Zabarmawan Kano na farko a tarihin Zabarmawan Kano, waɗanda suka shafe fiye da shekaru 170 suna zaune a birnin Kano.
Naɗin ya gudana ne a ranar Laraba da ta gabata a fadar Sarkin Kano, inda jama’a daga sassa daban-daban suka halarta domin shaida wannan muhimmin lamari na tarihi.
Masana tarihi da shugabannin al’umma sun bayyana wannan naɗi a matsayin wata babbar alama ta haɗin kai da girmama kowane rukuni da ke zaune a Kano ba tare da la’akari da asali ba.
Makusancin sabon sarkin, Alhaji Mustapha Abdulrazak, ya ce Sarkin Kano ya nuna adalci da hangen nesa ta hanyar amincewa da wannan sarauta, wadda za ta taimaka wajen haɗa kan Zabarmawa da sauran al’ummomin jihar.
Shugabannin ƙungiyoyin Zabarmawa sun bayyana cewa wannan sarauta za ta zama wata gada ta sadarwa tsakanin Zabarmawa da masarautar Kano, tare da taimakawa wajen warware matsalolin zamantakewa.
Sun kuma yi kira ga matasa ’yan Zabarmawa da su rungumi ilimi da sana’o’i domin ci gaban al’ummarsu da ma jihar Kano gaba ɗaya.
A jawabin karɓar sarauta, Sarkin Zabarmawan Kano ya yi godiya ga Allah da Sarkin Kano, tare da alƙawarin aiki tukuru wajen bunƙasa ilimi, lafiya da kasuwanci.
Ya ƙara da cewa zai yi aiki kafaɗa da kafaɗa da sarakunan gargajiya da shugabannin gwamnati domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa.
