APC ta ƙaddamar da rajistar katin mambobi ta intanet a Kano

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ta ƙaddamar da rijistar mambobinta ta zamani ta intanet, a wani taro da aka gudanar a dakin taro na Amani da ke Kano.

Shugabannin jam’iyyar sun bayyana cewa sabon tsarin zai taimaka wajen sauƙaƙa rijistar mambobi tare da kawar da matsalolin da ke tattare da tsohon tsarin hannu.

Shugaban jam’iyyar APC a jihar ya ce rijistar za ta ba da damar sanin sahihin yawan mambobin jam’iyyar a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Ya ƙara da cewa tsarin zai taimaka wajen inganta tsare-tsaren jam’iyyar na zaɓe da kuma tallafa wa mambobi a lokutan da suka dace.

An zaɓi matasa daga ƙananan hukumomi domin gudanar da rijistar, inda aka horas da su kan yadda ake amfani da na’urorin zamani da manhajojin intanet.

Wasu jiga-jigan jam’iyyar sun bayyana cewa wannan mataki alama ce ta yadda APC ke ƙoƙarin rungumar fasahar zamani domin ƙarfafa jam’iyyar.

Sun kuma yi kira ga mambobi da su fito su yi rijista domin tabbatar da haƙƙinsu a jam’iyyar.

By ukarofi