An kashe shanu masu yawa bayan zuba musu guba a wani gari a Filato, inji Miyetti Allah

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) ta fitar da rahoton cewa da yawan shanun ‘ya’yan ƙungiyar ana kashe su ta hanyar zuba musu guba a yayin da suke kiwo a ranar Juma’a da yamma a kusa da ƙauyen Kwi da ke ƙaramar Hukumar Riyom a jihar Filato.

Ibrahim Babayo, shugaban ƙungiyar a jihar ta Filato ne ya bayyana faruwar lamarin yana mai cewa a ranar Juma’ar da ta gabata an kashe musu shanu 6 a dai wannan ƙauye bayan sun yi zargin an zuba musu guba ne.

A cewar shugaban ƙungiyar MACBAN, ƙungiyar ta sanar da kwamandan shiyyar Operation Enduring Peace da ke ƙaramar Hukumar Barikin Ladi, wanda daga baya ya aike da jami’ansa domin zuwa wurin da abin ya faru.

Ya ce bai iya tantance adadin shanun da aka kashe ba izuwa yanzu saboda akwai sama da shanu 100 da suke kiwo a lokacin da abin ya faru a wurin wanda hakan ya sa su ba su iya tantancewa ba.

Shugaban MACBAN ya yi Alla-wadai da lamarin tare da kiran jami’an tsaro da su gagauta bincike don gano wanda ke da hannu a lamarin.

A lokacin da aka tuntuɓi muƙaddashin mataimakin mai magana da yawun rundunar ta 3 ta rundunar sojin Nijeriya, Aliyu Danja, ya ce, ba su da masaniyar faruwar lamarin duk da ganin jami’an rundunar a wurin da aka gani a wurin.

Danja, wanda laftanar janar ne, ya ce, rundunar sojin Nijeriya za ta bibiyi wannan lamari tare da sanar da manema labarai halin da ake ciki.

Shugaban MACBAN ya bayyana satar shanun da zuba musu guda da wani yunƙuri na takalar makiyaya a jihar.

“Abin da muke gani yana faruwa a kwanan nan, hujja ce ta irin yadda ake tura mu bango. Kuma duniya tana ganin abin da ke faruwa. Wasu mutane sun ce sai sun kashe mu a lokacin bikin Kirsimeti, kuma wannan ne ya sa suke cigaba da kashe makiyaya da dabbobinsu,” ya faɗa.

“Jami’an tsaro da suka haɗa da ‘yan sanda da SSS da rundunar ofureshan Enduring Peace suna ganin abin da ke faruwa da mu.”

“A ranar Larabar nan, an sace mana shanu sama da 160 da zuba wa wasu da dama guba. Mu mutane ne masu son zaman lafiya kuma muna cigaba da bin doka. Muna kira ga ‘ya’yan ƙungiyarmu da su kwantar da hankalinsu, su bari jami’an tsaro su binciki lamarin,” inji Babayo.

A lokacin da aka tuntuɓi shugaban ƙungiyar matasan ƙabilar Berom (BYM), Solomon Dalyop, ya ce ba su da masaniyar faruwar lamarin.

A cewarsa shugaban ƙungiyar, “Abin da zan ce shi ne Fulani su bar Fulato. Suna iƙirarin ana kashe musu shanu, amma da yamman nan sun tafi sun kashe mutane uku a Drong a Foron da yin awon gaba da shanu masu yawa. Sai dai ba za mu iya tabbatar da yawan shanun da aka sace ba a lokacin harin.”

By ukarofi