’Yan bindiga sun yi garkuwa da Fulani a Kogi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Wasu ’yan bindiga sun kai hari garin Jege da ke ƙaramar Hukumar Yagba ta Gabas da ke Jihar Kogi, inda suka sace wasu mazauna yankin, da ba a kai ga tantance adadinsu ba.

An ce mutane da dama ne aka tafi da su zuwa ma oyar miyagun da ke cikin dazukan yankin.

Rahotanni daga yankin a ranar Talata sun bayyana cewa ’yan bindigar kutsa cikin garin ne a tsakar daren Litinin, suna harbe-harbe.

Wani mazaunin garin Ejuku, maƙwabciyar Jege, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce: “Yanayin tsaro a Jege ya yi matuƙar munana tun da safiyar Talata. Mutane da dama ne aka sace a harin ’yan bindigar a daren Litinin.

“A halin yanzu ba zai yiwu a tantance adadin waɗanda aka sace ba. A cikin rudanin da ya lulluɓe al’ummar, mutane da dama sun tsere, wasu kuma har yanzu suna barin garin. Ba mu san wanda ya tsere ba, ko wanda aka sace a yanzu.”

Shugaban ƙungiyar Cigaban Jege (JDA), Oluomo JD Akogun, a cikin wata sanarwa da ya wallafa a dandalin sada zumuntar al’ummar yankin a daren Litinin, ya ce, “Rahoton da ya zo min shi ne cewa an kai hari wani sansanin Fulani da ke tsakanin Jege da Ejuku.

“Rahotannin harbe-harbe masu yawa sun mamaye garin Jege. An ce wasu daga cikin Fulani ne aka sace a harin da ’yan bindigar suka kai.”

Bincike da aka gudanar a ranar Talata ya nuna cewa fargaba ta mamaye mazauna yankin, inda da dama ke ta faman tuntubar ’yan uwansu da masoyansu domin tabbatar da halin da suke ciki.

Lokacin da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kogi, CSP William Aya, bai amsa kiran waya ko saƙon tes ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.

By ukarofi