Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (ICPC) ta ce za ta fara bincike nan take kan zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Mai na ƙasa (NMDPRA), Farouk Ahmed.
Hukumar ta bayyana cewa haka ne a yayin da sanar cewa ta karɓi takardar ƙorafin da Shugaban Kamfanin ɗangote, Alhaji Aliko ɗangote, ya shigar kan Farouk Ahmed.
Mai magana da yawun hukumar ICPC, John Odey, ya bayyana cewa za a gudanar da cikakken bincike kan ƙorafin. A ranar Talata ne attajirin ɗan kasuwar, ta hannun lauyansa, ya shigar da ƙorafi yana neman a kama tare da gurfanar da Shugaban na NMDPRA.
ɗangote ya zargi Farouk Ahmed da cin hanci da rashawa da kuma amfani da ƙarfin ofishinsa wajen almundahana da karkatar da kuɗaɗen gwamnati domin amfanin kansa, wanda hakan ke cutar da al’ummar Nijeriya.
Lauyansa, Dakta Ogwu Onoja, SAN, ya rubuta wasiƙar zuwa ICPC a madadinsa, ya ce yana da ƙwararan hujjoji da ke goyon bayan zarge-zargen da yake yi wa Ahmed.
ɗangote ya fara yin zargin ne a ranar Lahadi, a taron manema labarai da ya gudanar a Legas, inda ya zargi shugabancin NMDPRA ƙarƙashin Ahmed da daƙile ayyukan matatun mai na cikin gida, ta hanyar ci gaba da bayar da lasisin shigo da kayayyakin mai daga waje, “duk da ƙaruwar ƙarfin tace mai a cikin gida.”
A cewarsa, shigo da man daga ƙasashen waje na hana bunƙasar masana’antu a cikin gida, tare da samar da ayyukan yi a ƙasashen waje, yayin da ‘yan Nijeriya ke fama da matsalar masana’antu.
Daga bisani, Majalisar Wakilai ta ƙasa ta shiga tsakani a rikicin, inda ta gayyaci ɗangote da Ahmed domin nemo hanyar warware matsalar.
Sai dai duk da shiga tsakani da ’yan majalisar suka yi, ɗangote ya buƙaci ICPC da ta binciki Ahmed tare da gurfanar da shi, domin hakan ya zama darasi ga sauran mutanen da ake zargin suna yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon ƙasa.
Da yake mayar da martani ta cikin wata gajeriyar sanarwa, Odey ya ce: “Hukumar ICPC na sanar da jama’a cewa ta karɓi wata wasiƙar ƙorafi a hukumance a ranar Talata, 16 ga Disamba, 2025, daga Alhaji Aliko ɗangote ta hannun lauyansa.
