Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
An yi kira ga mata su riƙa daurewa suna yin karatun a fannin zayyanar gidaje da aka fi sani da ‘Architecture’ domin bayar da gudummawa ga bunƙasa cigaban al’umma.
Arc. Binta Ahmad Umar Darakta ta Park and Recreation Centre a Hukumar Tsara Birane ta Jihar Kano “KNUPDA” ta bayyana hakan da take zantawa da ‘yan jarida.
Ta ja hankalin mata su riƙa kwantar da hankalinsu wannan aiki na Architecture ba zai gagaresu ba da yardar Allah in sun shiga za su iya don haka su daina jin tsoron karatun fannin su daina ja da baya.
Ta yi nuni da cewa akwai ɓangaren da su mata ne yakamata su shigo ciki idan ba su da yawa waye zai yi? Don haka mata su dage kar su ji tsoro yadda kowane irin karatu yake haka nan na Architecture yake.
Ta ƙara da cewa kawai bambanci da wasu karatun shine yana da ɗan jan lokaci aikin, saboda za ka iya kwana ka yini kana zane amma cikin ikon Allah za ka ji shi ma ka fi so fiye da komai, shi yana buƙatar lokaci ne don haka ‘yan uwa mata a dage.
Arc. Hajiya Binta Ahmad Umar ta ce a matsayinta ta Architecture ta yi zane-zane da yawa, wasu na gidaje ne domin ta yi aiki a hukumar Ilimin bai ɗaya SUBEB a sashin Physical Planing, kuma tana alfahari dukkan ƙananan hukumomi na Kano ta je ta duba ayyuka na ajijuwa da banɗakuna da sauran ayyukan gine-gine da yawa.
Ta yi nuni da cewa a zamananta a hukumar SUBEB a nan ta daɗa samun ilimi na ƙwarewa da gogewa a aikin Architecture saboda kullum a cikin aiki ake.
Arc. Hajiya Binta Ahmad Umar wacce tsohuwar darakta Technical ce a hukumar gudanarwar Kasuwar Muhammad Abubakar Rimi da kasuwar Singa wace yanzu take Darakta ce Park and Recreation a hukumar tsara birane ta jihar Kano KNUPDA ta ce a baya lokacin da suka yi karatu babu mata a wannan ɓangare na Architecture da yawa amma yanzu abubuwa suna sauyawa ana ɗan samun masu yin karatu a fannin.
