Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) a ranar Alhamis ta ce, sojojin da aka tura sassa daban-daban na ƙasar sun kashe ’yan ta’adda 36, sun kuma kama ’yan bindiga 137 da kuma mara musu baya 6.
Rundunar sojin ta kuma ce, sojojin sun kama mutane 15 da suka yi satar mai tare da kwato kuɗi Naura 3,177,650.00 tare da kuɓutar da mutum 140 da aka yi garkuwa da su.
Daraktan yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba wanda ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, ya kuma bayyana cewa, an ƙwato jimillar makamai 37 da alburusai 370.
Ya bayar da bayanin abubuwan da aka awato kamar haka; “Bindigu ƙirar AK47 guda 16, 6 pump action guns, 6 dane guns, 3 fabricated rifles, ƙananan bindigogi ƙirar guda 6, 199 rounds of 7.62mm special, 6 rounds of 7.62mm NATO, 9 AK47 magazines and 2 G3 magazines, motoci 8, babura 45, wayoyin hannu guda 32, adduna 925.
“Sauran sun haɗa da: 61 dugout pits, kwale-kwale na katako 32, tankunan ajiya 87, jirgin ruwa mai sauri ɗaya, tukunya 32, 3 outboard engine, janareta ɗaya, wuraren tace fetur ba bisa aa’ida ba 36, lita 310,700 na satar ɗanyen mai.”
A cewar Janar Buba, a tsakanin 26 ga Yuli zuwa 1 ga Agusta, 2023, jimillar ’yan ta’adda 313 da suka haɗa da maza 12, mata 138 da kuma yara 162 sun miƙa wuya ga sojoji a wurare daban-daban.
Ya ce, a ranar 27 ga watan Yuli, sojoji sun yi wa ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP kwanton vauna a Shetimari da ke ƙaramar hukumar Konduga a Jihar Borno.
“Sakamakon haka, an kashe ’yan ta’adda 2, yayin aka ƙwato bindiga ƙirar AK 47 ɗaya, Mujallar bindigu ta AK47 guda 6, alburushi na musamman 7.62 mm da wayar hannu ɗaya aka samu,” in ji shi.
Kakakin rundunar ya ce, a ranar 30 ga watan Yuli, sojoji tare da haɗin gwiwar rundunar ‘yan sanda sun yi wa wasu da ake zargin ’yan ta’adda kwanton ɓauna ne a wani shingen bincike da ke ƙauyen Kubtara a ƙaramar hukumar Dikwa ta jihar Borno.
Ya bayyana cewa, bayan wani artabu da suka yi da ’yan ta’addan, sojojin sun kashe ɗan ta’adda guda ɗaya tare da kwato bindiga ƙirar AK 47 guda ɗaya, Mujallar bindiga ƙirar AK47 ɗaya da kuma harsashi na musamman 7.62 mm.
“A ranar 26 ga watan Yuli, biyo bayan rahoton sirri kan ayyukan ta’addanci a ƙauyen Hashime da ke aaramar hukumar Mafa a jihar Borno.
Sojojin sun gudanar da wani samame. An ceto mutane 5 da aka yi garkuwa da su tare da awato babur da sauran kayayyaki.
“A ranar 27 ga watan Yuli, biyo bayan rahoton sirri kan kutsawar wani fitaccen ɗan ta’addan da ke haɗa kayan aiki a cikin birnin Maiduguri. Sojojin sun gudanar da wani samame tare da kama su. Wanda ake zargin ya amince da cewa shi masinja ne da ke kai makamai da sauran kayayyaki ga ’yan ta’adda a mavoyarsu. Wanda ake zargin ya tabbatar da alaƙa da ƙungiyar ƙetare makamai,” inji shi.