Daga MUAZU HARDAWA a Bauchi
A ƙoƙarinta na ganin ta inganta ayyukan shari’a tare da rage cunkoso a gidajen yari, babbar Mai Sharia ta Jihar Bauchi Hajiya Rabi Talatu Umar ta fara rangadin gidajen gyaran tarbiyya na Jihar Bauchi don gane wa idonta yadda alƙalai ke gudanar da ayyukansu tare kuma da duba yiwuwar rage cunkoso a gidajen yari.
Ziyarar da ta fara a ranar Litinin ta ziyarci Darazo da Misau da Gamawa da Zaki da Azare da Ningi yadda a gidan gyaran tarbiyya na Gamawa ta ga matasa sama da 100 suna jiran shari’a.
Don haka ta nuna rashin jin daɗinta na ganin ƙananan matasa da basu wuce shekara 18 zuwa 30 ba su ne yawanci ke jiran hukunci. Don haka ta bayyana takaici tare da jan hankalin iyaye su tashi tsaye wajen lura da tarbiyyar yaransu.
Haka kuma su ma shugabanni ta ja hankalinsu kan su lura da halin da matasa suka shiga na aikata miyagun ayyuka, idan ba an tashi tsaye an magance matsalolin matasa ba nan gaba da su iya zama matsalar da za ta damu kowa.
Mai Shari’a Rabi Talatu Umar ta ziyarci Mai martaba Sarkin Misau Alhaji Ahmed Sulaiman mni, inda shi ma ya yaba game da ziyarar aiki da ta kawo masarautar, inda ya bayyana wannan aiki da Mai Sharia Rabi Talatu Umar ke yi sau uku ko huxu a shekara.
Ya ce lamarin na taimakawa wajen gano matsalar fannin shari’a da na gidajen gyaran tarbiyya don a magance.
Ya ce Misau gida ne a gareta duk lokacin da ta kawo ziyara sai an amfana da zuwanta. Don haka ya ja hankalin jama’a su ci gaba da addu’a don samun sauƙi daga irin mawuyacin halin zamantakewa da aka shiga a koma ga Allah don samun fita daga ciki, musamman ya yaba game da sanya ido da take kan ma’aikatan ta musamman alƙalai don ganin an yi wa al’umma adalci a lokacin da suke aikin su na shari’a.
Rabi Talatu Umar ta ƙalubalanci wasu alƙalai game da sakaci ko nuna rashin ƙwarewa kan aiki ta buƙaci su sameta a ofishinta a Bauchi don kurakurai da suka yi.