An rage wa Kano Pillars maki uku da tarar miliyan N9.5 bisa cin zarafin alƙalin wasa da wasu laifukan

Spread the love

Hukumar Gudanarwar Gasar Nigerian Premier League, NPFL ta ci tarar ƙungiyar Kano Pillars bayan wani hayaniya da ya ɓarke a yayin karawarta da Shooting Stars a mako na 8 da wannan kakar.

Akan haka ne Kano Pillars za ta biya Naira milyan 9.5, sannan za a zaftare mata maki uku da kuma haramta mata wasa a gida saboda rikici.

Hukuncin da aka ɗauka akan Kano Pillars shi ne kamar haka:

  1. Tarar Naira Miliyan Daya (₦1,000,000.00) saboda rashin samar da isasshen tsaro da inganci.
  2. Tarar Naira Miliyan Daya (₦1,000,000.00) saboda jefa abubuwa masu hadari zuwa cikin filin wasa da jifan jami’an wasa.
  3. Tarar Naira Miliyan Daya (₦1,000,000.00) saboda rashin tabbatar da ladabi da doka da magoya bayan kungiyar ke yi.
  4. Tarar Naira Miliyan Daya (₦1,000,000.00) bisa laifin rashin da’a da ya iya kawo rashin mutunci.
  5. Tarar Naira miliyan biyu (₦2,000,000.00) saboda cin zarafin ‘yan wasan da sukazo bakuncin wasa da jami’an wasa.
  6. Tarar Naira Miliyan Biyu (₦2,000,000.00) a matsayin diyya na jiyya da lahani da aka yi wa ‘yan wasan da jami’ai.
  7. Tarar Naira miliyan daya da dubu dari biyar (₦1,500,000.00) a matsayin diyyar Naira dubu dari biyu da hamsin ga kowanne jami’an wasan.
  8. Umarnin cire maki 3 ga Kano Pillars saboda cin zarafin jami’an wasan.
  9. Umurnin rufe filin wasa na Sani Abacha har abada, ga Kano Pillars FC, na sauran kakar wasan bana, ko kuma a kalla rasa buga wasanni goma a gida har sai kun tabbatar da cewa ba za a sake samun qfaruwar haka anan gaba ba.

A halin yanzu, Kano Pillars za ta buga wasanninta na gida a Katsina.

By Babaji