An tayar mana da mikin ciwo – Iyalan Marigayi Bello sun yi tir da afuwar Tinubu ga Maryam Sanda

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Iyalan Marigayi Bilyaminu Ahmed Bello, wanda matarsa, Maryam Sanda ta halaka a shekarar 2017, sun koka da yin alla-wadai da afuwar shugaban ƙasa da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa matar a ƙarƙashin ikon doka.

A wata takarda da Dakta Bello Haliru Mohammed (Ɗan Galadiman Gwandu) ya fitar a madadin iyalan, ƴan uwan marigayin sun bayyana matakin a matsayin abinda ya sabunta musu raɗaɗin rashinsa musamman duba da yadda aka yi ta ɗauki-ba-daɗi a yayin shari’ar al’amarin.

A cewarsa, iyalan sun zaɓi yin shuru da riƙe kansu tun lokacin faruwar al’amarin a ranar 19 ga watan Nuwamban 2017, saboda yadda suke kyautata wa harkar shari’ar Nijeriya zato wajen yin adalci.

Haka ko aka yi domin a ranar 27 ga watan Junairun 2020, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa, wanda Kotun Ɗaukaka ƙara da ta Ƙoli suka jaddada a 2020 da 2023.

Ya ƙara da cewa, duk da cewa mai laifin ba ta nuna nadama ba tun daga farkon shari’ar har ƙarshe, iyalan sun samu nitsuwa da hukuncin kotu tare da ɗaukar dangana akan iftila’in da ya same su.

Saidai, sun ce yafiyar shugaban ƙasar ga mutane 175 da aka yanke wa hukunci ciki har da na waɗanda nasu kisa ne, ya ta da wa mutane da dama mikin ciwo da kuma sanya alamar tambaya ga harkar shari’a a ƙasar.

By Babaji