Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Dukku/Nafada, Hon. Abdullahi El-Rasheed Bala, ya buƙaci gaggawar shiga tsakani daga gwamnatin tarayya domin gyara da sake gina hanyar Gombe–Dukku–Darazo, wacce ya bayyana a matsayin muhimmiyar hanya ta tattalin arziki da ke haɗa al’ummomi da dama a yankin Arewa maso Gabas.
Ɗan majalisar, wanda kwanan nan ya kai ziyarar gani da ido kan hanyar, ya ce manufar wannan ziyara ita ce duba halin da hanyar ke ciki da kuma tattara bayanai kai tsaye domin ƙarfafa tattaunawarsa da hukumomi da cibiyoyin raya yankin da abin ya shafa.
Hon. El-Rasheed ya nuna damuwarsa kan taɓarɓarewar hanyar, yana mai cewa ta zama abin wahala ga direbobi, ‘yan kasuwa da manoma waɗanda ke amfani da ita wajen jigilar kaya da amfanin gona tsakanin Gombe, Dukku, Darazo da sauran wurare.
Ya bayyana cewa gyaran hanyar zai taimaka wajen inganta zirga-zirga da tsaro, ƙara yawan samar da amfanin gona, bunƙasa cinikayya, samar da ayyukan yi ga matasa, da kuma farfado da tattalin arzikin al’ummomin da ke gefenta.
Hanyar Gombe–Dukku–Darazo ba hanya ce kawai ba; ita ce jijiya ta tattalin arzikin mutanenmu. Gyaranta zai buɗe manyan damar kasuwanci da inganta rayuwar dubban jama’a a yankin,” in ji shi.
Hon. El-Rasheed ya kuma sha alwashin yin aiki tare da Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, da hukumomin tarayya domin tabbatar da cewa aikin ya samu kulawa ta gaggawa da kuma kuɗaɗen da za su tabbatar da ɗorewarsa.
Ya bayyana cewa ya riga ya rubuta takarda zuwa ga hukumar raya Arewa maso Gabas (NEDC), inda ya roƙi hukumar da ta gaggauta shiga tsakani wajen gyaran da sake gina hanyar, wacce ta jima tana fama da lalacewa.
Yayin da yake sake jaddada ƙudurinsa na ganin an inganta hanyoyin sufuri, ɗan majalisar ya ce samar da hanyoyi masu kyau na da matukar muhimmanci wajen buɗe damar tattalin arzikin karkara da jawo jarin masu zuba jari zuwa Dukku, Nafaɗa da sauran yankuna.
A tuna cewa a ranar 7 ga Nuwamba, 2023, Hon. El-Rasheed ya gabatar da ƙudiri a majalisa mai taken “Buƙatar gyaran hanyar Gombe–Dukku–Darazo da Daukaka ta zuwa matsayin Truck A a jerin hanyoyin tarayya”, wanda ya samu yabo daga ‘yan majalisa saboda manufarsa ta ƙarfafa hada-hadar kasuwanci da dangantakar tattalin arziki a Arewa maso Gabas.
