
A kokarin bunkasa al’amuran da za su habaka gina rayuwar al’umma, kungiyar ‘yan kasuwa ta Bichi, Traders Multi-Purpose Cooperative Society Limited, ta samu ganawa da Sheikh Lawan Abubakar da Alh. Musa Yaro da Malam Isah Bala da kuma Hon. Sani Mukaddas Bardan Bichi.
Shugaban Kungiyar, Alhaji Abubakar Mazahim Sale ne ya sanar da haka ga manema labarai cewa Sheikh Lawan Abubakar, da ya kansance limamin babban masallacin Juma’a na Karamar Hukumar Bichi, ya ja hankalin ‘yan kasuwa su ci gaba da ba da hadin kai da goyon bayan dukkan al’amuran da za su ciyar da su gaba.
Haka kuma su zama masu mu’amala da koyi da addinin musulunci wajen siye da siyarwa tare da taimakon junansu, musamman marasa karfin cikinsu muddin suna da amana a harkokin gudanar da kasuwancinsu.
A yayin jawabinsa, tsohon Shugaban Kula da Hada-hadar Kudi na Kamfanoni Sheikh Isyaka Rabi’u, Alh. Musa Yaro, ya yi alkawarin taimaka musu ta hanyar gayyato manyan diloli daga manyan kasuwanni; Singa, Dawanau domin bai wa kananan ‘yan kasuwa kaya da suka hada da; suga, fulawa, taliya, makaroni, indomie da ma kayan kamfanin BUA da kuma sauran kamfanoni a kan farashin kanfani tare da kuma yi musu lamuni.
Sannan, ya yi kira da a lura da tsaftar kasuwanni da kuma kula da baki dake shigowa daga makwabtan jihohi.
A hannu guda kuma da Shugaban Kungiyar, Alhaji Abubakar Muzahim Saleh ya yaba da irin yadda Shugaban Asibitin Bichi, Pharm. Isah Bala da suka haɗa da; Sakataransa, Shugaban Sashen Kula da Kananan Asibitoci, Shugaban Ma’aikatan Asibiti na Shiyyar Bichi, Shugabar Ma’aikatan Jinya ta Asibitin Bichi da sauran ma’aikatan asibitin suke gudanar da ayyukansu.
Malam Isa shi ma ya yaba bisa irin yadda kungiyar kasuwar take kai ziyara bisa karbar shawarwari a dukkan wasu matakai na bunkasa harkokin cigaban jama’ar Bichi, har ma ya ja hankalinsu da su lura da tsaftar kasuwa da tabbatar da inganci da lafiyar kayan abinci.
Da yake jawabinsa, tsohon Shugaban Karamar Hukumar Bichi, kuma Shugaban Jam’iyyar APC na Kano ta Arewa, Hon. Sani Mukaddas Bardan Bichi, ya bayyana tsari da gudunmawar da suka bai wa kasuwar a lokacin mulkisa da kuma irin kudirin da yake da shi a kan kasuwar, bisa haka ya nuna jin dadinsa na yadda Allah ya kawo Dan Majalisar Tarayya, Alhaji Abubakar Kabir Abubakar, da ya sabunta kasuwar zuwa ta zamani.
Sannan ya yi alkawarin isar da korafe-korafen ‘yan kasuwar zuwa ga mahukunta domin daukar matakin da ya dace, ya kuma tabbatar da aniyar Dan Majalisa na taimaka wa ‘yan kasuwar, musamman ma wadanda suka rasa jarinsu, kamar yadda jami’ar yaɗa labaran ƙaramar hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta ruwaito.







