
Jihohin Arewa za su fuskanci zafin rana a wannan mako, kamar yadda NIMET, wato
Hukumar kula da yanayi ta ƙasa ta bayyana.
Ta ce, za a fuskanci ƙwala zafin ranar ne a sassa daban-daban na Nijeriya daga Litinin zuwa Laraba.
A cikin hasashen da hukumar ta fitar a Abuja, ta ce Arewa za ta fuskanci rana mai zafi da girgijen hadari, yayin da ake sa ran ruwan sama da iska a wasu sassan Taraba da Kebbi.
Daga bisani kuma, ana iya samun ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a wasu yankuna kamar Adamawa, Kaduna, Borno, Bauchi, Gombe, Kebbi da Kudancin Sokoto.
Hsashen ya kuma nuna cewa, za a samu ruwan sama a wasu sassan Niger, Benuwai, Filato da Kogi, yayin da Abuja, Kwara da Nasarawa za su fuskanci ruwan sama da yammaci.
A yankin kudu kuwa, hukumar ta ce za a samu ruwan sama musamman a jihohin Ogun, Ondo, Ekiti, Imo, Ebonyi da Abia da safe, sannan da yamma za a sami ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a yawancin jihohin kudanci.
Hukumar ta gargadi jama’a da su yi tuƙi da hankali yayin ruwan sama, su guji tsayawa ƙarƙashin manyan itatuwa, kuma su cire na’urorin lantarki daga socket don kauce wa haɗari.
