
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ASUU, ta yi watsi da umarnin gwamnati na kada a biya albashi ga mambobinta da suka shiga yajin aiki, yana mai gargaɗin cewa babu wata barazana da za ta sa su ja da baya.
Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ya bayyana hakan a wata hira da gidan talabijin na Channels inda ya ce a shirye suke su cigaba da bin tsarin tattaunawa, amma ba za su lamunci kama karya daga ɓangaren gwamnati ba wajen ƙoƙarin raina ikon fannin ilimi.
ASUU ta shiga cikakken yajin aiki na makonni biyu tun a ranar Lahadi, bayan ta zargi gwamnati da gaza cika alƙawuran da ta daɗe tana yi.
Saidai gwamnatin tarayyar ta ce ta riga ta biya yawancin buƙatun ASUU, tana mai bayyana yajin aikin a matsayin marar hujja.
Haka kuma ta yi barazanar aiwatar da manufar ‘ba aiki, ba albashi’.
Kungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta yi watsi da wannan barazana, tana mai cewa hakan zai iya lalata tsarin tattaunawa mai adalci, tare da nuna goyon bayanta ga ASUU.
Piwuna ya bayyana cewa ya samu kiran waya daga shugaban tawagar tattaunawar gwamnatin tarayya, Alhaji Yayale Ahmed, da kuma sakon Ministan Ƙananan Ayyuka, waɗanda suka nuna an ba su umarni su shiga tsakani.
“ASUU tana shirye. Muna jiran kiran hukuma domin mu zauna mu tattauna mu warware matsalar gaba ɗaya”, inji Piwuna.
Ya ƙara da cewa ƙungiyar ta yi yajin aiki ne a matsayin matakin ƙarshe bayan dogon lokaci ana jiran gwamnati ta cika alƙawura.
Piwuna ya ƙalubalanci gwamnatin da ta ce duk matsalolin an warware su, yana mai tambayar dalilin da yasa ake sake shirya tattaunawa idan haka ne.
