
Iran ta ƙaddamar da munanan hare-hare akan matatar mai mafi girma a Saudiyya, wadda rukuni ce ta kamfanin Saudi Aramco.
Wannan hari dai wani ɓangare ne da zai bunƙasa rikicin da ya ɓarke a yankin Gabas ta Tsakiya tsakanin Iran da haɗakar Amurka da Isra’ila.
Rahotanni sun ce an yi amfani da jiragen sama marasa matuƙa musamman samfurin Shahed-136, wajen kai harin a safiyar yau Litinin.
Harin ya haifar da gobara a matatar man, amma hukumomin Saudiyya sun bayyana cewa an yi nasarar shawo kan gobarar kuma ba a rasa rayuka ba.
Sakamakon harin, Saudi Aramco ta dakatar da ayyuka a matatar ta Ras Tanura a matsayin matakin tsaro yayin da ake tantance ɓarnar da al’amarin ya haifar.
Farashin ɗanyen mai ya yi tashin gwauron zabi da kusan kaso 10 nan take bayan samun labarin farmakin.
Rundunar tsaron Saudiyya ta sanar da cewa ta samu nasarar kakkaɓo wasu karin jiragen marasa matuƙa da suka yi ƙoƙarin kai hari kan wasu wuraren a yankin gabashin kasar.
A watan Satumbar 2019, an taɓa kai wani gagarumin hari akan cibiyoyin Abqaiq da Khurais wanda ya dakatar da kusan rabin man da Saudiyya ke samarwa a lokacin.
