Mai ba gwamna shawara kan harkokin siyasa kuma tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Katsina Rt Hon Yau Umar Gwajo Gwajo yace tausayi da kuma kyakkyawan shugabanci na Malam Dikko Umar Raɗɗa ne yasa ake gudanar da shirin ciyarwa da raba abinci ga al’umma domin mutane su samu damar cigaba da gudanar da azumi cikin aminci.
Rt Hon Gwajo Gwajo ya bayyana hakan ne yayin wata zantawa da manema labarai a ofishin sa.
A cewar sa bana Allah ya kawo sauƙi ta hanyoyi daban daban da yasa al’ummar musulmi a jihar Katsina suke gudanar da azumi cikin sauƙi, gwamna Dikko Raɗɗa na cigaba da gudanar da tallafawar da ya saba domin talakawa su samu sauƙi.
“Abun a yaba ne yadda ko wane gari a faɗin jihar ake dafa abinci domin raba wa ga marassa ƙarfi.”
Gwajo Gwajo yace hakan yasa al’umma na cigaba da addu’oi ga jihar katsina da ƙasa baki ɗaya wanda hakan yasa mutane ke cigaba da ganin yadda ake zaman lafiya ke cigaba da dawowa a jihar katsina.
Gwajo Gwajo sai a ƙarshe ya yi kira ga al’umma da su yi amfani da wannan lokaci na azumin watan ramadan domin addu’oi ga jihar katsina inda ya bayyana cewa babu abinda yafi ƙarfin addu’a.
Ya kuma yaba wa shugabannin ƙananan hukumomi, yan majalisar ƙasa da na jiha, manyan jami’an gwamnati da sauran masu hannu da shuni da su ma suka bi sahun Dikko Raɗɗa wanna raba tallafin kuɗi da kayan abinci ga mabuƙata.
