JAMB ta fara rajistar DE ta 2026

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Samar da Gurbin Karatu a Makarantun Gaba da Sakandare (JAMB) ta fara sayer da fom ɗin neman gurbin karatu a jami’o’i, wato ‘yan ‘Direct Entry’ na zangon karatun 2026.

JAMB ta bayyana haka ne a wani rubutu da ta wallafa ta kafar X inda ta ce an fara rajistar ne da yau Litinin, 2 ga watan Maris, 2026, yayin da za a rufe a Rane Asabar, 25 ga Afrilu, 2026.

Hukumar ta nanata cewa za ta karɓi rajistar ne daga dukkan ofisoshinta da ke sassan jihohin Nijeriya da ta amince da su a hukumance.

Hakan na nufin ta bai wa ɗaliban da ke takardun shaidar kammala karatu damar a wasu makarantu yin rajista domin samun gurbi kai-tsaye a jami’o’i.

Shaidar cancantar ta haɗa da na “National Diploma, National Certificate in Education, Interim Joint Matriculation Board, A-level certificates, or other approved equivalents”, kamar yadda NewsPointNigeria ta ruwaito.

An fara rajistar ne kwanaki kaɗan da kammala na UTME, wanda aka rufe a ranar 28 ga watan Fabrairu.

By Babaji