Ramadana: Rundunar ‘yan sanda a Kano ta haramta tashe saboda tsaro

Spread the love

Rundunar ‘yan sanda a Jihar Kano ta sanar da dakatar da wasan Tashe na shekara-shekara da aka saba gudanarwa a watan Ramadana saboda dalilan matsalolin tsaro.

A wata sanarwa da Kakakinta, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Asabar, rundunar ta ce an ɗauki matakin ne tare da haɗin-gwiwar Gwamnatin jihar dom tabbatar da kare zaman lafiyar al’umma a lokacin azumi.

A cewarta, matakin zai taimaka wajen hana ɓata-gari yin amfani da bukukuwan wajen aikata laifuka kamar daba, ƙwacen wayoyin hannu da kuma shan miyagun kwayoyi.

Rundunar ta tabbatar wa mazauna jihar cewa an tanadi isassun matakan tsaro domin dakile irin wadannan ayyuka tare da tabbatar da gudanar da Ramadan cikin lumana.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori ya bukaci iyaye, masu kula da yara da ɗaukacin jama’a da su bai wa jami’an tsaro haɗin kai wajen gargaɗin ‘ya’yansu da waɗanda ke ƙarƙashinsi akan kauce wa aikata duk wani abu da ka iya kawo tsaiko ga doka da oda.

Ya kuma yi gargadin cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci bisa tanadin doka.

Rundunar ‘Yansandan ta kuma taya al’ummar Jihar Kano murnar watan Ramadan, tare da yi musu fatan azumi mai albarka da nasara.

An shawarci mazauna jihar da su tuntubi rundunar ta lambobin gaggawa kamar haka: 08032419754, 08123821575, 08076091271, da 09029292926, ko kuma ta manhajar “NPF Rescue Me” da ake samu a Google PlayStore, domin bukatar gaggawa.

By Babaji