
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Litinin Majalisar ‘Yan sanda ta Ƙasa ta tabbatar da Olatunji Disu a matsayin sufeto janar na rundunar.
An yi haka ne a zaman majalisar da Shugaba Bola Tinubu ya kira a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Bayan haka, Shugaban ƙasar zai kuma tura sunan Disu ga Majalisar Dattawa domin tantancewa.
Kakakin Shugaban Ƙasa Bayo Onanuga ya tabbatar da al’amarin ga jaridar PUNCH bayan zaman, wanda aka shafe tsawon mintina 40 ana yi.
Zaman majalisar abu ne da doka ta hukunta, kamar yadda yake a kundin dokokin ‘yan sanda na 202p, wanda ke bayar da dama ga mambobin majalisar su yi nazari akan naɗin.
A ranar Talatar da ta gabata ne Fadar Shugaban Ƙasar ta sanar da murabus ɗin Kayode Egbetokun daga muƙamin a wata sanarwa.
Majalisar ‘yan sanda tana gudana ne ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa, wadda ta ƙunshi gwamnonin jihohi 36 da shugabannin Hukumar Kuka da Lamuran ‘Yan sanda da sufeto janar na rundunar a matsayin mambobi.
