
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ICPC, ta sanar da gano wasu na’urori da ake zargin na naɗar bayanan sirri ne da takardu masu muhimmanci akan lamuran tsaro a gidan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da ke Abuja.
A cikin takardun da ta gabatar a gaban kotu, ICPC ta bayyana cewa na’urorin na da fasahar da za ta iya kutsawa cikin tattaunawa ta sirri tare da tattara muhimman bayanan tsaro.
Hukumar ta bayyana cewa, an gudanar da binciken ne acikin gidan a gaban iyalansa, Hadiza El-Rufai, da ɗansa, Mohammed Bello, inda aka ƙwato kayayyakin da ake zargi.
Lamarin na daga cikin matakan bincike da hukumar ke amfani da su yayin da ake sa ran kotu za ta cigaba da sauraron shari’arsa domin tantance gaskiyar zarge-zargen da ake da su akansa.
ICPC ta ce tana da zarge-zarge masu alaƙa da rashawa akan tsohon gwamnan ciki har da ɓatar wasu maƙudan kuɗaɗe da adadinsu ya kai Youro miliyan 1.4; jimillar biya guda 180 da aka yi na zargi da kuɗinsu ya kai N2,158,799,199 daga kuɗaɗen haraji da aka tattara na Jihar Kaduna.
Haka kuma an tura wasu kuɗaɗe ga asusun da ba a iya tantance su ba da jimillar adadinsu ta kai N428,122,180.18 da dai sauransu.
