An sake zaɓar Laporta a matsayin shugaban Barcelona zuwa 2031

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewa an sake zaɓen Joan Laporta a matsayin shugaban FC Barcelona bayan ya samu gagarumar nasara a zaɓen da aka gudanar a ƙarshen makon da ya gabata.

Laporta ya samu ƙuri’u 32,934 wanda ya kai kashi 68.18, inda ya doke babban abokin hamayyarsa Víctor Font mai ƙuri’u 14,385, wato kaso 28.78.

Hasashen farko daga kafafen yada labarai na Cataloniya sun bayyana cewa da fari alamu sun nuna Laporta ne zai lashe zaɓen.

Dubban mambobin ƙungiyar, waɗanda ake kira socios, sun fito domin kaɗa ƙuri’arsu, lamarin da ya ba Laporta damar sake jagorantar Barcelona na shekaru biyar masu zuwa a babbar ƙungiyar ta ƙasar Sifaniya da ma nahiyar Turai.

By Babaji