
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da Taiwo Oyedele a matsayin ƙaramin ministan kuɗi.
Shugaban ya rantsar da shi ne a jiya Litinin a wani taƙaitaccen bikin rantsuwar da ya gudana a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
A makon da ya gabata ne Majalisar Dattawa ta tabbatar da Oyedele a matsayin ministan bayan Tinubu ya naɗa shi.
Haka kuma, a ranar 3 ga Maris ne Tinubu ya miƙa sunan Oyedele ga majalisar a wata takarda da ya aike wa Shugabanta, Sanata Godswill Akpabio inda ya buƙaci a tabbatar da shi a muƙamin kamar yadda sashe na 147(2) na kundin tsarin mulkin 1999 ya tanada.
Kafin yanzu, Oyedele ya kasance shugaban kwamitin shugaban kasa akan manufofin kasafin kuɗi da sake fasalin haraji, wanda ya jagoranci yin garambawul ga tsarin harajin Nijeriya.
Oyedele ya maye gurbin Dakta Doris Uzoka-Anite, wacce aka mayar da ita Ma’aikatar Kasafin Kuɗi da tsare-tsaren Tattalin Arziƙi a matsayin ƙaramar minista.
