An sako mutumin Kano, Mubarak Bala da aka tsare a kurkuku bisa ɓatanci ga addini

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wani mazaunin Kano mai suna Mubarak Bala ya samu ƴanci daga gidan yari bayan shekaru huɗu da aka tsare shi bisa laifin ɓatanci.

Mubarak Bala mai shekaru 40 an maka shi a kotu ne sakamakon samun sa da laifuka 18 na wasu abubuwa da ya wallafa a shafin Facebook a shekarar 2020.

A lokacin da BBC take hira da shi, Mubarak ya ce an yi ta nuna damuwa kan halin da yake ciki daga masoya da makusanta.

Nijeriya dai ƙasa ce da ta bada muhimmanci matuƙa game da lamuran da suka shafi addini, don haka ne yasa ake hukunta duk wanda ya yi ɓatanci ga Musulunci ko Kiristanci.

Ɓatanci dai wani al’amari ne na shari’a a dokar musulunci wanda ake aiki da shi a jihohi 12 na Nijeriya wanda aciki akwai Kano, haka kuma laifi ne a kundin dokar manyan laifuka ta Nijeriya.

A shekarar 2014 ne Mubarak ya karɓi addinin Musulunci a lokacin da ya ke kurkuku a karon farko a Kano, inda har ya yi ta samun fargabar rasa ransa daga ƴan uwansa fursunoni a sanadiyyar haka.

Da farko dai an yanke masa hukuncin shekaru 24 ne a gidan yarin inda daga bisani bayan ɗaukaka ƙara da lauyoyinsa da iyalansa suka yi, ya sa aka rage wa’adin zuwa shekaru huɗu.

An kama Mubarak ne, wanda ɗaya ne daga cikin masu tsokaci kan harkokin addini bayan wasu lauyoyi sun shigar da ƙara ga ƴan sanda kan wasu abubuwan da ya wallafa a soshiyal mediya.

By ukarofi