Sojoji shida da ƴan ta’adda 34 sun mutu a harin sansanin sojoji a Borno – Hedikwatar Tsaro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hedikwatar Tsaro (DHQ) ta tabbatar da mutuwar ƴan ta’adda 34 da sojoji 6 sakamakon wani hari a sansanin sojoji dake Sabon Gari a ƙaramar hukumar Damboa a Jihar Borno.

Daraktan yaɗa Labarai, Manjo-Janar Edward Buba ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya ce kawo yanzu ba a bayyana sojojin da suka rasa rayukan nasu ga iyalansu ba wanda za a yi hakan a hukumance nan ba da jimawa ba.

Edward Buba ya ce ƴan ta’addar sun kai harin ne a wani yunƙuri na ramuwa sakamakon kashe wani kwamandansu da sojoji suka yi.

A lokacin da ƴan ta’addar suka hari sansanin, kwatsam ba tare da sun yi aune ba sai jami’an sintiri da suke dawowa daga aiki suka farmake su tare da haɗin-gwiwar waɗanda ke sansanin.

Dakarun sun haɗa da na haɗaka (CJTF) da ƴan Banga da jami’ai na musamman wato ‘hybrid forces’ inda suka sha ƙarfin mayaƙan ƴan ta’addan tare da kashe wasu daga cikinsu da kuma kora su daga yankin.

Ya ƙara da cewa, a lokacin da ƴan ta’addan suke ƙoƙarin guda ne sai jami’an atisayen HADIN KAI na sojojin sama suka yi ta ruwan alburusai akan su.

Ya kuma ce dakarun sun ƙwato makamai da dama waɗanda ciki akwai AK47 guda 23 da alburusai ƙirar 7.62mm guda 200.

Har’ilayau, ya yi kira ga ƴan jaridu da su girmama tsarin da hukumar take bi wajen bada bayanai.

Kazalika, ya ce jami’an za su cigaba da ƙoƙarin kawo ƙarshen ta’addanci a shiyyar Arewa-maso-Gabas da ma Nijeriya baki ɗaya.

By ukarofi