Mai ba gwamnan Kano shawara ya rasu kwana ɗaya da rantsar da shi

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Sabon mai bai wa gwamnan Kano shawara kan ayyuka, Injiniya Ahmad Ishaq Bunkure ya rasu, kwana ɗaya da gwamna Abba Kabir Yusuf ya rantsar da shi a gidan gwamnati.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya rabawa manema labarai, marigayin ya rasu a yau Laraba a ƙasar Masar.

Ya ce Gwamna Yusuf, wanda ya nuna kaɗuwa ga rasuwar Bunkure, ya bayyana mutuwar ta sa a matsayin babban rashi ga iyalinsa da ma Kano baki ɗaya.

“Wannan wani yanayi ne na kaɗuwa da alhini saboda Injiniya Bunkure mutum ne mai hazaƙa da sanin makamar aiki wanda jihar Kano za ta amfani da shi.

” Allah ya gafarta masa ya bai wa iyalinsa da mu baki ɗaya hakurin rashin sa,” in ji gwamnan Kano

By ukarofi