An sanya lokacin ƙaddamar da littafin tarihin fitattun ‘yan Jihar Kano 24

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

A cigaba da shirye-shiryen ƙaddamar da littafin “Mu San Magabata”, wanda Kabiru Ahmad Ƙwalli ya rubuta.

Littafin wanda ya ƙunshi tarihi da muhimmiyar rawa da waɗannan mutane suka taka wajen ci gaban jihar a fannoni daban-daban.

A yayin zaman ƴan kwamitin da ya gudana a Mustibrah Polytechnic da ke Kano, Ƙwalli ya ce manufarsa ita ce cike gibi wajen rubuce rubucen tarihi, ganin cewa yawancin manyan mutanen Kano ba su da cikakkun kundin tarihin rayuwarsu, duk da gagarumar gudummawar da suka bayar.

Littafin ya yi duba ne kan shugabanni, malamai, yan kasuwa da jajirtattun masu hidima ga al’umma da suka yi fice a tarihi. Fitattun sunayen da suka fito a littafin sun haɗa da:

Madakin Kano Shehu Ahmad, Alƙalin Kano Umaru, Sheikh Sani Auwalu Darma, Alhaji Uba Ringim, Alhaji Imam Wali, Alhaji Ado Dandolo,
Malam Nura Alƙali, Malam Adamu Aminu.

Sauran sun haɗa da: Kansila Malam Ahmadu Rufa’i Daura, Alhaji Barau Maiwake, Alhaji Baballe Ila, Alhaji Baffa Yola, Alhaji Muhammadu ‘Yankwashi Kazaure, Alhaji Mahe Bashir Wali, Alhaji Salisu Sambajo da Alƙali Husaini Sufi da dai sauran sanannun jaruman al’umma har zuwa mutum 24.

Kwamitin ƙarƙashin jagorancin Farfesa Bashir Yusuf, tare da Alhaji Ibrahim Aminu Dan’Iya a matsayin mataimaki, ya sanya satin farko na karamar Sallah mai zuwa a matsayin ranar ƙaddamar da wannan muhimmin littafi.

Kazalika, kwamin ya ce zai cigaba da kai ziyarori ga muhimman mutane a Kano kafin wannan rana, duka dai don ganin wannan ƙaddamarwar ta samu nasara, wanda
daga nan sai littafin ya shiga hannun al’umma.

By ukarofi