
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Alƙalin alƙalan Nijeriya (CJN), Mai Shari’a Ibrahim Tanko Muhammad ya rasu a wani asibiti da ba a bayyana ba.
A cewar wata majiya da ta gana da ShaharaReporters a safiyar yau Talata, tsohon alƙalin ya rasu ne yayin da ake masa magani a wani asibitin ƙasar waje.
“Tsohon CJN Tanko Muhammad ya rasu. Ya rasu ne a safiyar nan a wani asibitin Saudiyya “, inji majiyar.
Tuni ƙungiyar ɗaliban shari’ar Musulunci ta ƙasa (NAMLAS) ta miƙa saƙon ta’aziyyarta, inda ya bayyana hakan a matsayin babban rashin ga fannin shari’a da ma addini musulunci baki ɗaya.
Alƙali Tanko Muhammad ya yi aiki a ƙarƙashin fannin shari’a a Nijeriya na tsawon shekaru, wanda har ya kai ga CJN. Ya yi murabus ne a watan Yunin 2022 sakamakon matsala da ta shafi kiwon lafiyarsa.
