
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta ce adadin hauhawar farashi a Nijeriya ya ragu da kaso 14.45 cikin 100 a watan Nuwamban 2025.
NBS ta bayyana hakan ne a wani rahoton na ‘Consumer Price Index (CPI)’ da ta fitar a ranar Litinin, inda ta nuna cewa wannan shi ne karo na takwas a jere da hauhawar farashi ke raguwa a shekarar 2025.
Rahoton ya nuna cewa wannan raguwa ta zarce burin Shugaba Bola Tinubu na kashi 15 cikin ɗari, abin da ke nuna alamun samun sauƙi a matsin tattalin arziƙi.
A cewar hukumar, adadin hauhawar farashi a watan Nuwamba ya yi ƙasa idan aka kwatanta da kashi 16.05 cikin ɗari da aka samu a watan Oktoba, 2025.
Masana na ganin wannan ci-gaba na iya taimakawa wajen rage tsadar rayuwa da kuma farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasa, idan aka cigaba da wannan yanayi.
