
Rundunar ƴan sanda a Jihar Neja, ta sanar da kama wata mata mai suna Zuwaira Usman, mai shekaru 35, ’yar Pandogari a Karamar Hukumar Rafi, bisa zargin ƙwarewa wajen jigilar alburusai ga ’yan ta’adda a jihar.
A wata sanarwa, rundunar ta ce an cafke wadda ake zargin ne a ranar 4 ga Nuwamba, 2025, da misalin ƙarfe 5:00 na yamma, bayan samun sahihan bayanan sirri. Jami’an FID–STS na rundunar ne suka aiwatar da kamen.
A yayin bincike, Zuwaira ta amsa cewa ta hadu da wani mutum mai suna Lawali a Birnin Gwari, Jihar Kaduna, a watan Satumba 2025, inda suka yi musayar lambobin waya. Daga baya Lawali ya bukace ta da ta yi tafiya zuwa Warri a Jihar Delta domin karɓo masa wani kaya, inda ya ba ta kuɗin mota naira dubu ashirin (₦20,000).
Ta ce bayan isarta Abuja, Lawali ya tuntubi direban motar tare da umartar inda za a sauke ta a Warri. A can Warri, ta hadu da wani mutum mai babur mai suna Ahmed, wanda ya miƙa mata wani buhu dauke da flask, tare da umartar ta da ta kai wa Lawali. An kuma ba ta ƙarin kuɗin mota naira dubu talatin (₦30,000) domin dawowarta Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa bayan Zuwaira ta dawo ta hanyar Abuja zuwa Kaduna, ta mika kayan ga Lawali a Birnin Gwari. Daga bisani bincike ya nuna cewa flask ɗin na dauke da alburusai 2,500 na bindigar AK-47.
Rundunar ’yan sandan ta ce an kama Ahmed a Jihar Delta, yayin da ake ci gaba da farautar Lawali, tare da zurfafa bincike domin bankado sauran masu hannu a lamarin.
Rundunar ta jaddada kudirinta na ci gaba da yaki da ta’addanci da safarar makamai, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro hadin kai ta hanyar bayar da bayanan sirri.
