An umarci kwamishinan ‘yan sandan Zamfara ya binciki shari’ar ɓata suna da mataimakin gwamna ya yi

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

A cigaba da zaman sauraron ƙarar da tsohon Ɗan Majalisar Jihar Zamfara ya shigar na ɓata masa suna da mataimaki na musamman ga Gwamna Dauda Lawal kan yaɗa labarai, Mustafa Jafaru Kaura, a Kotun Majistare ta daya a Gusau, Hon. Yusuf Alasan Kanoma, kotun ta umarci Kwamishinan ‘yan sandan Jihar da ya gunanar da bincike kan batun.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Murtala Abdullahi ya bayyana hakan a yau Laraba.

Lauyan wanda yake ƙara Barrister Surajo Garba Gusau ya bayyana hakan ga manema labarai jim kaɗan bayan sauraron ƙarar.

A cewar sa, bisa umarnin da kotun ta bayar, hakan ya nuna za a tabbatar da adalci ga wanda yake ƙarar watau Hon. Yusuf Alasan Kanoma.

A cewar sa, dalilin bayar da umarnin da kotun tayi, ya biyo bayan bada umarnin kama wanda ake ƙara tunda ya kasa bayyana a gaban kotun.

Yana mai nuni da cewar hakan yasa a zaman kotun karo na Uku, wanda ake ƙara ya gurfana a gaban ta.

Barr. Gusau ya Kara da cewa, zasu ci gaba da biyyayya ga kotun har sai an tabbatar da adalci a shari’ar.

“Zamu cigaba da bibiyar ƙarar tare da biyyayya ga umarnin kotun domin a tabbatar da adalci ga wanda yake ƙara watau Hon Yusuf Alasan Kanoma”. Yace

Tuni dai Kotun ta dage sauraron karar har zuwa Ashirin ga wannan Watan nan Mayu domin samun cikakken bayani daga Kwamishinan Yan Sandan Jihar don cigaba da sauraron karar tareda yanke hukunci.

By ukarofi