Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta ware Naira Biliyan 1.99 don sayen man dizal domin samar da wutar lantarki ga gidan Fadar Shugaban ƙasa a shekarar 2025.
Wannan na zuwa ne yayin da aka samu jinkirin aikin samar da lantarki mai amfani da hasken rana na Gwamnatin Tarayya wanda aka shirya zai fara aiki tsakanin Disamba 2024 da Janairu 2025.
An tattaro cewa, Gwamnatin Tarayya ta biya miliyan N88.75 don sayen man dizal a rubu’in farko na shekarar 2024.
Binciken da aka yi kan GoɓSpend, wani dandalin fasaha na jama’a da ke bin diddigin yadda gwamnatin tarayya ke kashe kuɗaɗe, ya nuna kuɗaɗen dizal da suka kai miliyan N88.75 tsakanin 15 ga Maris zuwa 20 ga Mayu, 2024.
A ranar 15 ga Maris, 2024 an biya miliyan N40.77 ga Kamfanin Emmahaly Petroleum Limited na lita 30,000 na dizal da aka kawo wa asibitin fadar shugaban ƙasa da gidan mai na mataimakin shugaban ƙasa; da miliyan N12.46 zuwa A.Y.M. Shafa Limited na lita 10 na dizal (kamar yadda aka nuna a cikin takardar) wanda aka kawo wa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Gidan Gwamnatin Tarayya.
ƙudirin kasafin kuɗin 2025 ya ware Naira biliyan 1.99 don buƙatun gidan gwamnati na dizal ɗin janareta.
