Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Funmilayo Ransom Kuti ta kasance mace ɗaya tilo a jerin sunayen ‘yan gwagwarmayar neman ‘yancin kan Nijeriya. Fumilayo ta kasance malamar makaranta, ’yar siyasa, mai fafutukar kare ’yancin mata sannan kuma mai riƙe da sarautar gargajiya. Ita ce mahaifiya ga shahararren mawaƙin nan na Nijeriya, Femi Kuti.
Funmilayo ce mace ta farko da ta fara tuƙa mota a Nijeriya. An zaɓe ta a majalisar sarakunan gargajiya, inda ta kasance wata wakiliya ta al’ummar Yarabawa. Fafutukar da ta yi ta janyo wa ’ya’yanta baƙin jini musamman lokacin gwamnatocin soji.
Cif Fummilayo Ransome-Kuti: (Mahaifiyar Fela Kuti) Abubuwa 11 da ya kamata a sani game da mace ta farko da ta tuƙa mota a Nijeriya;
1. Cif Funmilayo Ransome-Kuti, mace ta farko da ta fara tuka mota a Nijeriya, malama ce, mai fafutukar siyasa, mai fafutukar kare haƙƙin mata kuma mai faɗa a ji a Nujeriya.
2. Ta kasance mai Tafiye-tafiye mai hazaka. Ta yi balaguro zuwa ƙasashe da yawa a duniya.
3. Kafin Nijeriya ta samu ‘yancin kai – musamman lokacin yaƙin cacar baka (Cold War) ta yi tafiya zuwa tsohuwar USSR, Hungary da China, inda ta haɗu da Mao Zedong – ɗan juyin juya halin gurguzu.
4. Ziyarar da ta yi zuwa ƙasashen da ke yankin Gabas ya fusata gwamnatin Nijeriya ta ‘yan mulkin mallaka, da kuma gwamnatocin Birtaniya da Amurka.
5. A shekarar 1956, gwamnati ba ta sabunta fasfo ɗin ta ba, saboda an yi imanin cewa manufarta ita ce ta rinjayi ’yan Nijeriya musamman mata da ra’ayoyi da manufofin gurguzu.
6. An kuma hana ta bizar Amurka saboda gwamnatin Amurka ta yi zargin cewa ita ’yar gurguzu ce.
7. Ta kasance daya daga cikin wakilan da suka yi shawarwarin samun ’yancin kan Nijeriya da gwamnatin Birtaniya.
8. Ta kasance wadda ta lashe kyautar zaman lafiya ta Lenin. Gwamnatin Soɓiet ta na bada kyautar ga fitattun mutane, fitattun ’yan gurguzu da magoya bayan Tarayyar Soɓiet waɗanda ba ’yan Soɓiet ba.
9. A cikin Fabrairu 1978, an jefar da ita daga tagar wani bene mai hawa 3 (Jamhuriyar Kalakuta) mallakar ɗanta mawaƙi, Fela. Hakan ya faru ne lokacin da sojoji dubu suka mamaye ginin. Ta suma kuma daga baya ta mutu a ranar 13 ga Afrilu 1978, daga raunin da ta samu daga faɗowar.
10. Wani lokaci a cikin 2012, don a mutunta ta, ana ɗauki hotonta domin bugawa a kan takardar kuɗi na N5000. Daga baya gwamnatin Nijeriya ta janye shawarar buga Sabon kuɗin N5000.
11. Bayan rasuwarta, ɗan nata Fela ya kai akwatin gawar ta zuwa Barrack Dodan – fadar mulkin Nijeriya a wancan lokacin kuma hedikwatar koli na sojan Nijeriya ya bar ta a bakin gate. Yayi hakan ne domin wulaƙanta gwamnatin mulkin soja da Obasanjo ya jagoranta saboda mamaye masa kadarori da ya yi sanadiyyar mutuwar mahaifiyarsa. Wannan mamayewa ya zaburar da Fela wajen yin waƙa mai suna “Coffin for Head of State”.
