
Daga BELLO A. BABAJI
Kotun Ɗaukaka ƙara ta Jihar Legas ta ƙi amincewa da buƙatar babban lauyan Nijeriya (SAN), Femi Falana, na haramta wa jami’an gwamnati zuwa ƙasashen waje neman magani.
Ta ce, hakan wani nau’i ne na tauye haƙƙin ɗan-adam da dokar ƙasa ta bayar na amince wa jami’an gwamnati da waɗanda ba su ba zuwa ƙasashen waje neman magani.
A watan Yulin 2010 ne Falana ya maka Gwamnatin Tarayya a kotu inda ya ke neman a tabbatar da samar wa al’umma asibitoci da sauran wuraren kula da lafiya masu inganci da kayan aiki isassu domin kula da lafiyarsu, inda ya ce rashin hakan saɓa wa dokar ƙasa ne.
Ya nemi wata kotu da ta umarci gwamnati ta gyara asibitoci da sanya kayan aiki aciki, wanda yin hakan zai hana jami’an gwamnati zuwa kowacce ƙasa da sunan neman magani da ake biya daga aljihun gwamnati.
Saidai, kotun ta yi watsi da buƙatar babban lauyan kasancewar ta ci karo da sashe na 6 (6) na kundin dokar ƙasa.
Kasancewar Falana bai gamsu da hukuncin ba ya sa ya ɗaukaka ƙara a shekarar 2021 da kuma ranar 30 ga watan Junairu na 2025, inda a yayin hukunci ne, kotun ta bayyana cewa abinda Falana ya faɗa na rashin kyan asibitocin Nijeriya da yawan mace-mace haka ne, amma hakan ba shi zai sa ta yi hukunci saɓanin doka ba, don haka sai ta ƙi amincewa da buƙatar.
A yayin da ya ke tsokaci game da hukuncin a wata takarda, Falana ya ce kotun ta gaza yin la’akari da wariya da ke tsakanin jami’an gwamnati da suke zuwa waje neman magani da kuma talakawa da ake bari suna mutuwa a asibitocin da ba su da wadatattun kayan aiki.
