Gwamnan Ribas ya bada sabon umarni bayan hukuncin Kotun Ƙoli kan ƙananan hukumomi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya ce za a sake gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar.

Hakan ya biyo bayan rushe zaɓen ne da Kotun Ƙoli ta yi, wanda aka gudanar a ranar 5 ga watan Oktoba, 2024.

A wata hira da gidan talabijin, Fubara ya tabbatar wa al’umma cewa gwamnatinsa za ta bi umarnin doka.

Don tabbatar da ƙananan hukumomin sun cigaba da aiki yadda ya kamata, gwamnan ya umarci Jagororin Hukumar Ƙananan Hukumomi ta jihar da ta karɓe iko a ƙananan hukumomi 23 dake jihar, waɗanda za su yi hakan ne a matsayin riƙon ƙwarya zuwa lokacin da za a sake zaɓen.

Ya kuma umarci ciyamomi masu barin gado da su miƙa ragamar shugabancin ƙananan hukumominsu ga jagororin hukumar a ranar 3 ga watan Maris.

Haka kuma, Fubara ya yi kira ga al’umma da su kwantar hankulansu tare da cigaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum cikin salama, ya na mai cewa gwamnatinsa za ta cigaba da girmama doka da oda.

By Babaji