
Daga BELLO A. BABAJI
Rundunar ƴan sandan Jihar Bauchi ta ce ta kama wani mai suna Alhaji Nuru Isa ɗan shekara 50 bisa tuhumar sa da amfani da bulala wajen zane matarsa mai suna Wasila Abdullahi, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarta.
Lamarin ya faru ne a kusa da makarantar kwalejin mata da ke Unguwar Fadaman Mada a jihar.
Kakakin rundunar, CSP Ahmed Wakil a wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce sun samu rahoton aukuwar lamarin ne da misalin ƙarfe 11:30 na dare a ranar 1 ga watan Maris.
Ya kuma ce, al’amarin ya biyo bayan saɓani ne da aka samu a tsakanin mijin, wanda ɗan kasuwa ne a kasuwar santiral dake cikin garin Bauchi da matarsa mai shekaru 24 game da kula da kayan abinci da ababen marmari da za a yi buɗe baki da su, wanda daga baya ya rikiɗe zuwa fito-na-fito a tsakanin su.
CSP Wakil ya ce, bayan dukan nata da ya yi ne sai ta yanki jiki ta faɗi, wanda hakan yasa aka yi saurin garzayawa da ita Asibitin Koyarwa na Jami’ar ATBU, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarta.
Ya ƙara da cewa, rundunar ta fara gudanar da bincike akan haƙiƙanin abinda ya faru yayin da suke tsare wanda ake zargi da aikata laifin.
