An yaba wa Gwamnan Kano kan matakan da yake ɗauka na inganta harkar filaye

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano 

An yaba wa gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf bisa irin matakai da take bijirowa da su na tabbatar da gaskiya a harkar hada-hadar filaye a tsakanin al’umma.

Shugaban kamfanin hada-hadar filaye, gidaje, gonaki da kangwaye na A.A. Nasara Universal Serɓices, Alhaji Auwalu Nasiru ne ya yi yabon da yake zantawa da ‘yan jarida.

Ya ƙara da cewa zuwan wannan gwamnati sun ji daɗi da irin matakai da ta bijiro da su ƙarƙashin ma’aikatar ƙasa na ganin ana gudanar da harkokin mallaka da sayar da gidaje da gonaki da filaye cikin tsari na tsafta da bin doka domin daƙile ɓatagari a harkar.

Ya ce a matsyinsu na masu sana’ar filaye hakan zai ƙara inganta sana’arsu ta yadda za a kawar da ɓata garin cikin harkar. Sannan a shirye suke su bai wa manufofin gwamnati na inganta harkar filaye, gonaki da kangwaye haɗin kai da goyon baya.

Ya ja hankalin shugabanni da yan ƙungiyar masu sana’arsu su cigaba da haɗa kai da manufofin gwamnati domin kare kima da mutuncin sana’arsu.

Shugaban kamfanin na AA Nasara, ya ce  za su cigaba da biyayya ga masarautar Kano ƙarƙashin Khalipha Muhammad Sanusi ta ganin ba su bayar da haya ko sayar da gidaje ga ɓatagari ba ta haɗa kai da masu unguwanni da dagatai dama jami’an tsaro da kullum suke  basu kulawa wajen gudanar da sana’ar su bisa tsari da bin dokoki.

By ukarofi