Atiku ya soki ‘samamen’ da jam’ian tsaro suka kai majalisar dokokin Jihar Legas

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya yi tir da kutsen da jami’an tsaro suka yi wa majalisar dokokin jihar Legas.

A shafinsa na ɗ, Atiku ya bayyana alamarin a matsayin abin ƙi, ya kuma ce wajibi ne a gudanar da cikakken bincike.

A cewarsa, ”abin takaici ne jami’an tsaron suka kai samamen da niyyar tilasta sauya shugabancin majalisar.”

Ya ce zargin gayyatar jami’an tsaron wajen sasanta rikicin majalisa lamari ne da bai kamata a lamunta ba kuma a yi bincike kansa da gaggawa inda ya ce hakan wani mataki ne na cutar da dimokraɗiyya.

Atiku ya kuma yi kira ga shugaba Tinubu ya mayar da hankali kan fito da Nijeriya daga matsalar da ya jefa ta maimakon ya rika katsalandan cikin alamuran jihohi.

A ranar Litinin ne aka wayi gari da wani sabon ruɗani a majalisar dokokin jihar ta Legas, lamarin da ya kai ga cewa jami’an tsaro sun yi wa harabar majalisar ƙwanya bayan raɗe-raɗin da ake yi kan cewa shugaban majalisar da aka tsige zai shiga majalisar a gobe Talata.

Hakan na zuwa ne bayan matakin da ‘yan majalisar suka ɗauka a kwanakin baya na tsige shugaban majalisar, Mudashiru Obasa, tare da zaɓen Mojisola Meranda a matsayin sabuwar shugabar Majalisar.

Wani bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda jami’an tsaro suka toshe hanyar shiga harabar majalisar, inda ‘yan majalisa suka yi cincirindo a wajen.

Wannan ya tursasa wa ‘yan majalisar yin zama a wani lambu da ke kusa.

By ukarofi