Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wata kotun soji ta yanke wa wani ƙaramin jami’in soja hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun sa da laifn kashe buduwarsa.
Kotun da ta zauna a Hedikwatar Runduna ta 82 da ke Enugu, ta yanke wa Priɓate Adamu Mohammed hukuncin kisa kan laifin budurwarsa mai suna Hauwa Ali.
Da yake sanar da hukuncin, Shugaban kotun, Birgediya Sadisu Buhari, ya ce, “Kotun Soja ta ƙasa ta yanke hukuncin cewa sojan da ake tuhuma, mai lamba 21NA/80/6365 Priɓate Adamu Mohammed, an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa tuhumar kisan kai.”
Muƙaddashin kakakin Rundunar, Jonah Unuakhalu, ya ce kwamitin kotun ya cimma matsaya ɗaya bayan nazari mai zurfi na shaidu, tarihin aikin wanda ake tuhuma, da kuma roƙon sassauci daga lauyansa.
Ya shaida wa manema labarai a Abuja cewa kotun sojan, ta kuma yanke wa wani Soja mai suna Priɓate Abubakar Yusuf hukuncin ɗaurin shekaru 10 a kurkuku saboda samun sa da laifin fashi da makami a wani shahararren kantin sayayya a Enugu.
Ya ƙara da cewa, an yanke wa waɗannan mutane biyu hukuncin ne bayan kammala shari’o’insu kan laifukan kisan kai da fashi da makami.
Babban Kwamandan Runduna ta 82, Manjo-Janar Oluyemi Olatoye, ne ya ƙaddamar da kotun sojin a ranar 18 ga Fabrairu, 2025, domin yanke hukunci kan shari’o’in da suka shafi jami’an da suka yi kuskure a cikin rundunar.
A cewarsa, waɗannan hukunce-hukuncen sai sun samu tabbatarwa daga hukumomin soji da suka dace, wanda ya nuna ƙarshen shari’o’in sojojin.
Ya sake jaddada ƙudurin Sojojin Nijeriya na tabbatar da ɗa’a da kuma kiyaye mafi girman ƙa’idoji na zabi’u da ƙwarewa.
“Kuskuren ayyukan wasu kaɗan ba su nuna ƙimar ƙungiyar ba. A koyaushe ana ɗaukar matakai masu sauri da kuma ƙarfi don tabbatar da riƙon amana da adalci,” inji shi.
