Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Meta, babban kamfanin Facebook ya bayyana cewa a cikin 2024, ya goge shafukan bogi sama da miliyan 100 a kan Facebook.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis, kamfanin ya ce ya kuma rufe sama da shafuka miliyan 23 masu satar basira.
Ta kuma jaddada cewa, daƙile shafukan bogi da masu satar basira a dandalinta na daga cikin ƙoƙarinta na inganta ƙwarewar masu amfani da Facebook.
Meta ya sanar da wani gagarumin yunƙuri don rage ayyukan da ba su dace ba a kan dandamalin sa da nufin ƙirƙirar ingantaccen yanayi mai mahimmanci ga mutane.
“Mun himmatu wajen sanya harkokin Facebook”.
Ya ƙara da cewa yana kuma ƙara matsa lamba wajen don yaƙi da masu satar basira.
“Wasu asusu suna ƙoƙarin yin amfani da algorithm na Facebook don kwaikwayon wasu, domin samun kuɗi.
