An yanke wa sojoji hukuncin ɗaurin rai da rai kan sayar wa ƴan ta’adda makamai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A wani yunƙuri na tsaftace ayyuka acikin jami’an sojoji, wata kotun sojoji da ke Maiduguri ta yanke wa wasu sojoji guda huɗu hukunci bisa samun su da hannu a cinikayyar makamai da alburusai tsakanin su da ƴan ta’adda.

Rahotanni sun bayyana cewa hukuncin, wanda aka yi a sashen jami’an atisayen Haɗin Kai na hedikwatar rundunar, ya aika saƙon gargaɗi ga dukkan jami’an tsaro da suke taimaka wa abokan gaba.

Birgediya Janar Mohammed Abdullahi, wanda ya gabatar da shari’ar ƙarƙashin jagorancin Janar Ugochukwu Unachukwu, ya ce jami’an sun wulaƙanta kakinsu sannan sun ci amanar ƴan Nijeriya.

An samu Sajent Raphael Ameh da laifin shirya makirci, satar alburusai da haramtattun cinikayya. Rahotannin banki sun nuna cewa akwai hada-hadar zargi a asusunsa sama da 100 tun daga watan Yulin shekarar 2022 zuwa Yunin 2024, lamarin da ya sa aka yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai.

Sai Sajent Ejiga Musa, wanda aka same shi da sayar da bindigar AK-47 da babban akwatin alburusai ga ƴan ta’adda, inda ya karɓi sama da N500,000, wanda shi ma aka yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai.

Na ukun su shine Lance Corporal Patrick Ocheje, wanda aka tura aiki a wani sansani a yankin Molai, inda ya sauya akalar wasu alburusai na faɗan ƙabilanci kuma ya sace bindigar abokin aikinsa da taimakon wani jami’in ɗan sanda, wanda shi ma hukuncin ɗaurin rai-da-rai aka yanke masa.

Sai na ƙarshensu, wato Coppola Rufus, wanda aka kama da sayar da alburusai guda 40 ƙirar 7.62mm ga wani ɗan sanda. Shi kuma hukuncin shekaru 15 aka yanke masa.

By Babaji