Majalisar Katsina ta amince da ƙudirin hukunci mai tsanani ga masu ƙwacen waya

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina ta amince da ƙudirin yin hukunci mai tsanani ga masu ƙwacen waya ta amfani da makami tare da buƙatar kirkiro da Jami’an tsaron Al’umma CWC a cikin ƙaramar hukumar Katsina.

Ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina Hon. Aliyu Abubakar Albaba ya gabatar da ƙudirin, a zaman majalisar ƙarƙashin jagorancin mataimakin kakakin majalisar Rt. Hon. Abdul Jalal Haruna Runka.

Da yake gabatar da jawabinsa yayin da yake gabatar da ƙudirin, Hon.Aliyu Abubakar Albaba ya bayyana cewa gabatar da ƙudirin ya biyo bayan yawaitar ƙwacen waya da makami a cikin garin Katsina, dake cikin ƙaramar hukumar Katsina.

Duk a zaman majalisar, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Zango Rt. Hon. Tasi’u Maigari Zango ya gabatar da ƙudirin hana taron bikin gama makaranta.

Kamar yadda mai gabatar da ƙudirin ya bayyana, yace” gabatar da ƙudirin ya zama wajibi duba da yadda taron bikin kammala makaranta ke ƙoƙarin ɓata tarbiyar ‘ya’yan mu, kuma ya kasance abun bai yi dai dai da ɗabi’un mu ba da koyarwar addinin mu, da kuma al’adar mu ba.

Shima, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Dutsi Hon. Abdul Jalal Isma’il Dutsi ya gabatar da ƙudirin gyara wutar lantarki ta garin Ɗan Aune da ke cikin ƙaramar hukumar Dutsi.

Hon. Abdul Jalal Isma’il Dutsi ya ci gaba da bayyana cewa” Saboda tsawon lokaci da aka ɗauka na lalacewar wutar sanadiyar faduwar turakun wutar, hakan ya sanya an sace wayoyin wuta da dama.

Bayan gabatar da ƙudirorin, majalisar ta tattauna a kan su, daga ƙarshe majalisar ta amince da ƙudirorin, inda Kakakin majalisar ya umurci akawun majalisar da ya tura ma ɓangaren zartarwa domin ɗaukar matakin da ya dace.

By ukarofi