Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Bayanai daga yankin ƙauyen Meradake ƙaramar hukumar mulki ta Augie sun bayyana cewa ranar Litinin ɗin da ta gabata ne waɗansu mutane ɗauke da manyan bindigogi suka yi ɗauki-ba-daɗi da wani shahararren ɗan sa-kai a kan hanyar garin Mera zuwa Zaggi da ke kan iyakar jihohin Kebbi da Sakkwato.
Wata majiya mai tushe daga ƙauyen ta shaida wa wakilinmu da cewa shi dai wannan ɗan sa kai da ba a bayyana sunansa ba yana kan babur ne sanye da kayan sa kai yana kan hanyarsa ta dawowa gida sai waɗansu mutane ɗauke da bindigogi saman babura suka biyo shi, yayin da fahimci suna bin sa ne sai ya sami waje ya tsaya bayan da suka zo sai suka bude masa wuta shi kuma sai ya mayar da martani inda cikin haka ne ya samu nasarar harbe mutum ɗaya a kai sauran sai suka gudu kafin mutanen gari su zo.
Majiyar ta ƙara da cewa wanda aka kashe ɗin dai bafullatani ne amma dai ba wanda ya san shi sai dai ana sa ran yana daga cikin Lakurawa saboda haka tuni ‘yan sa kai ɗin sun miƙa gawar ga sojoji da ke aiki a wannan yankin.
Waɗansu majiyoyi daga yankin sun bayyanawa wakilinmu da cewa har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto dai ba wani bayani daga hukumomin tsaro akwai jami’an tsaro na sojoji da aka girke a makarantar firamare da ke garin Mera sai dai ba su taɓuka komai.
Wakilinmu ya nemi jin ta bakin shugaban ƙaramar hukumar mulki ta Augie Honarabul Yahaya Muhammed Augie sai dai yana Saudiyya.
