Shugaba Tinubu ya gaza cika fatan ‘yan Nijeriya na samun kyakkyawan shugabanci – Dr Hakeem

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon mai ba wa Shugaba Tinubu shawara ta musamman kan harkokin siyasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce, gwamnatin Tinubu ta gaza wajen inganta rayuwar al’umma da harkokin mulki.

Baba-Ahmed ya ce, saɓanin manufar shugaban ƙasa da yake da’awa ta sabunta fatan ‘yan Nijeriya, rayuwar al’umma ta ƙara taɓarɓarewa ne a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.

Tsohon mai magana da yawun ƙungiyar dattawan Arewa ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels a ranar Talata.

“A zahiri yake cewa gwamnatin Tinubu ta cika wa al’umma fatan da suke da ita a kanta saɓanin iƙirarin cewa zai inganta shugabanci a Nijeriya,” ya faɗa.

A cewarsa, cire tallafin man fetur da Tinubu ya yi ya yi matuƙar tasiri wajen shafar rayuwar al’umma.

Ya ce, duk da cewa ba abu ne mai yuwuwa ba shugaban ƙasa ya sake dawo da tallafin man fetur ɗin ba, amma akwai buƙatar ya magance “asarar ma’adanai da ake yi” wanda ke tauye abin da jihohi da ƙananan hukumomi ya kamata su samu daga rarar cire tallafin man fetur.

Baba-Ahmed ya ce, shugaban ƙasa ya kamata ya ƙara ƙaimi wajen tabbatar da ana yin komai a buɗe a gwamnatinsa da sauran matakai na shugabanci da ake da su.

“Akwai ɓarnar albarkatunmu da ake yi da amfani da su ba bisa ƙa’ida ba da cin hanci da rashawa mai yawa da ke faruwa.”

Ya kuma koka kan yadda shugabannin ƙasa tun 1999 da ke maye gurbin gwamnatin da suka gada ke fin na bayansu taɓarɓarewa.

“Nijeriya na cikin mawuyacin hali, duk da kasancewar muna mulkin dimokraɗiyya ne. Wannan manufar ita ce kare albarkatun Nijeriya domin gina ƙasa da al’umma za su mora.”

“Tun 1999, kowanne shugabanci da ya zo sai ka tarar ya fi na baya lalacewa. Idan ka fara daga shekaru 7 na tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ina ga a gaskiya, ya yi ƙoƙari, amma wasu masu sukarsa sun ce, ya ɓata rawarsa da tsalle bayan da ya nemi wa’adi na uku.”

“Hawan shugaban ƙasa ‘Yar’Aduwa kan mulki ya kwantar mana da hankali. Ga shi mafi ƙarancin shekaru, ga hangen nesa da ƙarfi, sai dai abin kaico shi ne bai wuce shekaru biyu ba a kan shugabancin.”

“Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya karɓi mulki tare da jan gwamnatinsa a ƙasa. Mun yaƙi Jonathan saboda muna ganin Nijeriya ta canci ta samu shugaba mai nagari. Amma ba mu sani ba ashe za mu ɗora wanda bai cancanci ya shugabanci al’umma ba ne.”

“Shugaba Janathan bai yi shugabanci nagari ba, shi kuma shugaba Buhari kuma ba ma mulki ya yi ba kwata-kwata ba.”

A yanzu, muna da shugaba wanda ya fara a gurgunce, “wanda yake cewa, “yanzu lokacinsa ne da zai yi shugabanci.”

“Ko da ma mun yasar da maganar da ya yi, za mu ga bayan shekaru da fara shugabancin Shugaba Tinubu, yanzu za mu iya yin alƙalanci da abin da ya yi.”

“Za su gaya maka cewa ƙididdigar bankin duniya ya nuna cewa suna ƙoƙari, da duk wani ƙiyasi na duniya, amma ba wannan ne kaɗai ma’auni na auna gwamnati ba. Ana ana gwamnati ne da yadda al’ummarta ke rayuwa, kuma idan wannan ne ma’auni na yanke wa gwamnati hukunci, a fili yake cewa, gwamnatin shugaba Tinubu ta gaza daga sa-ran da al’umma ke yi na inganta tsarin shugabanci sama da na tsohon shugaban ƙasa Buhari,” ya faɗa.

By ukarofi